Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar ta Iran Bahram Kasimi ne yayi wannan kiran a lokacin da yake magana kan zagayowar shekaru 47 da sanya wuta da sahyoniyawan suka yi wa masallacin na Kudus inda yayi Allah wadai da ayyukan da sahyoniyawan suke yi na ruguza masallacin na Kudus.
Don haka sai kakakin ma'aikatar harkokin wajen na Iran ya kirayi cibiyoyin kasa da kasa da su dau matakan da suka dace wajen kare masallacin na Kudus, wanda ya kasance alkiblar farko na musulmi kana kuma waje na uku mafi tsarki na musulmin daga kokarin rusa shi da sahyoniyawan suke yi.
Har ila yau kuma kakakin Ma'aikatar harkokin wajen na Iran yayi kakkausar suka ga hare-haren baya-bayan nan da sojojin haramtacciyar kasar Isra'ila suka kai Zirin Gaza inda ya ce wadannan hare-hare suna nuni da siyasar wuce gona da iri da kuma bakar aniyar da sahyoniyawa suke da ita, kana kuma wata alama ce da ke nuni da tsaka mai wuyan da suke ciki sakamakon shan kashin da suke fuskanta a hannun dakarun gwagwarmaya.288