A sanarwar da kungiyar ta NDA ta fitar a shafinta na internet ta ce ta ajiye makamai kuma zata tattaunawa da gwamnati don ci gaban kasar kamar yadda mahukuntan kasar suka bukata a kwanakin baya.
Sanarwar ta ce 'yan avengers na bukatar zama teburin tattaunawa da gwamnati tare da halartar wakilan kasar da kuma wakilan kasa da kasa.
Wannan na zuwa ne bayan shafe watannin takwas na kai hare hare kan cibiyoyi da butututai mai da 'yan kungiyar ta NDA keyi a yankin Neja Delta lamarin daya hadasa mumunan koma baya ga tattalin arzikin kasar.288