Wasu majiyoyin labarai a Nigeria sun bayyana cewa kungiyar Boko Haram ta watsa wani sabon hotunan Vedio na yan mata yan makarantan Chibok wadanda ta sace tun watan Afrulin shekara ta 2014.
Kamfanin dillancin labaran AFP ya ce a safiyar yau Lahadi ne aka watsa hotunan Vedion inda wani mai magana rufe da fuskansa yake cewa wasu yan matan sun mutu a hare haren sama wadanda sojojin Nigeria suka yi ta kai masu. Mai maganan bai bayyana yawan yan matan da suke raye ba. Fiye da yan mata yan makaranta 200 ne kungiyar Boko Haram ta sace a shekara ta 2014 a lokacin da suke rubuta jarrabawa a makarantar.
Duk da cewa kungiyar ta Boko haram ta yi garkuwa da mutane da dama a cikin yakin da ta kaddamar a arewa maso gabancin tarayyar Nigeria amma sacewar yan matan Chibok ya fi jan hankalin kasashen duniya.288