A yayin ganawar, Zarif da Erdogan sun tabo muhimamn batutuwa da suka danganci alaka a tsakanin kasashen biyu, da kuma wasu batutuwan da suke da alaka da halin da ake ciki a yankin gabas ta tsakiya.
Haka nan kuma Zarif ya gana da Firayi ministan kasar ta Turkiya Binali Yeldmir, daga kashe kuma ya gudanar da taron manema labarai tare da takwaransa na kasar Turkiya Jawish Auglo, inda suka jaddada wajabcin yin aiki kafada da kafada a tsakanin Iran da Turkiya wajen shawo kan matsaloli da dama a yankin, da kuma kara bunkasa alaka ta tattalin arziki da cinikayya a tsakaninsu.288