Shugaban komitin bincike kan kisan da sojojin Nigeria suka yiwa yayan kungiyar harka Islamia a birnin Zaria na jihar Kaduna ya mika rahotonsa ga gwamnan jihar Nasir El-Rufai. Justice Mohammad Lawal Garba shugaban komitin a yayin mika rahoton ya bayyana cewa komitin ya sami bayanai daga wurare 3500, sai dai bangaren Harka Islamia bata halarci zaman ba amma wani mai bawa kungiyar shawara ya sami halattan zaman.
A nashi bangaren gwamnan jihar kaduna Nasir El-rufai ya ce zai baje rahoton ga jama'a bayan tantance bangaren da suke da matsalar tsaro. Zai kuma bayyana matsayin gwamnati daga dangane da rahoton da kuma matakan da zata dauka don haka aukuwar irin haka nann gaba.288