Yayin jawabi ga al’ummar kasar shugaba Hollande ya bayyana tsawaita dokar ta bacin dake shirin karewa na watanni uku.
Shugaba Francois Hollande cikin halin kaduwa yace an kai wannan hari ne a ranar da Faransawa ke bikin ranar yancin kan su, kuma cikin wadanda harin ya ritsa da su har da kananan yara.
Hollande ya bayyana damuwa kan yadda za’ayi amfani da mota dan hallaka wadanda ke walwalar su, inda yake cewa kasar ba zata bada kai bori ya hau ba, a yaki da ta’adanci da kuma karfafa aikin da suke a Iraqi da Syria wajen yaki da ISIS.
Shugaban ya sanar da kara wa’adin dokar ta baci na watanni uku da kuma kiran sojin wucin gadi dan inganta tsaro a kasar.
Wannan dai shine hari na uku cikin watanni 18 a kasar, kuma yana zuwa ne sa’oi kadan bayan shugaban kasar yace ba zasu tsawaita dokar ta bacin da ke shirin karewa ranar 26 ga wata ba.288