26 Yuni 2016 - 18:32
Ma'aikatar Kula Da Lamuran Addini A Masar Ta Hana Malaman Kasar Zuwa Iran

Ma'aikatar kula da ayyukan addini a masar ta hana malaman addinin kasar zuwa Iran

Ma'aikatar lamuran addinin na kasar Masar ta yi gargadi ga malaman addini da kuma mahaddatan Al'Qur'ani mai girma wadanda suke zuwa kasar Iran don gabatar da shirye shirye na ramadan ko wasu ayyuka da su daina koma kuma ma'aikatar ta dauki mataki a kansu.

Muryar jumhuriyar musulunci daga birnin Alkahira ya nakalto jaridar " الشرق الاوسط" ta kasar Saudia wacce ake bugawa a birnin Londan tana cewa daga yanzu duk wani limamin masallan jama'a ko makarancin al-qur'ani da ye tafi kasashen waje ba tare da yardar ma'aikatar addini na kasar ba zai rasa aikinsa sannan hukuncin ba zai tsaya nan ba.288