23 Yuni 2016 - 19:40
Sojojinn Kasar Iraqi Sun Kara Kusantar Birnin Musil A Wasu Sabbin Nasarorin Da Suka Samu Kan Daesh

Sojojin kasar Iraqi sun kara samun nasarori a kan kungiyar Daesh a fafatawan da suke yi da su a cikin lardin Ambar.

Sojojin kasar Iraqi sun kara samun nasarori a kan kungiyar Daesh a fafatawan da suke yi da su a cikin lardin Ambar. Majiyar sojojin kasar Iraqi ta bayyanawa tashar television ta Presstv mai watsa shirye shiryensa da harshen turanci a nan Tehran cewa sojojin kasar sun kara nosawa zuwa gaba a kokarin da suke yi na dawo da ikon gwamnatin kasar a birnin Musil birni mafi girma na biyu a kasar Iraqi.
Tun cikin watan Yunin shekara ta 2014 ne mayakan kungiyar yan ta'adda ta Daesh suka kwace iko da birnin Musil daga arewacin kasar.
Priministan kasar ta Iraqi Haider al-Abadi ya yi alkawarin cewa kubutar da birnin Musil daga hannun yan ta'adda yana kusa.
A wani labari daga yammacin lardin ambar kuma, sojojin sama na kasar ta Iraqi sun yi luguden wuta kan wata mabuyar Daesh a yankin, inda da dama daga cikin su kungiyar suka halaka.288