12 Yuni 2016 - 15:32
Gwamnatin jihar Kaduna ke da alhakin aika-aikar da 'yan daba suka yi a Gyallesu

A wata takardan manema labarai da aka rarraba dauke da sa hannun Malam Ibrahim Musa, shugaban bangaren yada labaru na Harkar Musulunci a Nigeria karkashin jagorancin Sheikh Ibraheem Yaqoub El-Zakzaky, ya bayyana gwamnatin jihar Kaduna a matsayin wadda keda alhakin aika-aikar da wasu 'yan daba suka

Yi a unguwar Gyallesu a farkon wannan wata na Ramadan bayan agajin kayayyakin abinci da Sheikh El-Zakzaky ya bada umurnin a aiwatar kamar yadda aka saba a ko wacce shekara.

Takardar tayi bayani abin da ya faru daki daki, sannan ta bayyana yadda ita gwamnatin ta jihar Kaduna ta zaku taga ta shafawa Harkar Musulunci kashin kaji ta yadda zata cire tausayawar da al'umma suke yi mata.

A wannan karon ma yana daya daga cikin munanan yunkurin nata na ganin an haifar da hargitsi kan wannan kyakyawan aiki na alheri da Malam ya saba yana gabatarwa a duk shekara.

Malam Ibrahim Musa a karke yayi kira ga gwamnatin jihar Kaduna data dauki matakin kama wadanda suke da hannu kan wannan aika-aika, sannan kuma ta hukumta su gwargwadon laifin su, kuma a biya diyya da hasara ga al'umma da aka ci zarafin su a lokacin wannan aika-aikar, in tana so ta wanke kanta daga zargin da ake yi.