Kakakin ‘Yan Sandan Jihar Charlse Muka ya ce jami’an soja sun harbe biyar daga cikin masu fafutukar bayan sun kai hari kan ‘Yan Sanda suka kuma kashe biyu daga cikin su, tare da raunana wasu.
Rahotanni sun ce masu fafutukar sun kuma kai hari kan matafiya a hanyar Asaba zuwa Onitsha.
Amma ‘Yan sanda sun cafke wasu da dama daga cikinsu a Jihohin Enugu da Imo da ke yankin kudu masu gabashi.288