21 Afirilu 2016 - 10:35
Syria : MDD Ta Fara Kwashe Mutane A Wuraren Da Ake Rikeda

MDD ta fara aiwatar da wani tsarin ta na kwashe da mutane marasa lafiya ko kuma masu rauni a wuraren dake karkashin ikon 'yan tawaye ko kuma sojojin gwamnati a kasar Syria.

Wannan tsarin dai ya shafi mutane 500 a cikin birane hudu na kasar kamar yadda wata majiya daga MDD a birnin Damascos ta shaidawa kanfanin dilancin labaren Faransa na AFP.

Tuni dai aka fitar da wasu matasa fararen hula 15 da kuma sofafi 10 da yammacin jiya Laraba a yankin Zabadani wanda ke karkashin ikon 'yan tawaye a yammacin Damascos.

Kazalika wata majiya soji ta shaida cewa za'a fitar da wasu mutane 225 a kusa da Madaya.

A farkon wannan watan ne jagoran shirin, Jan Egeland ya bayyana wa manema labarai cewa za'a kaddamar da wani gagarimin shiri na kwashe marasa lafiya da kuma masu rauni a yankunan da suka hada da Madaya, da Zabadani dake karkashin ikon sojoji da kuma Foua da Kefraya da 'yan tawayen ke rikeda a arewa maso yammacin kasar ta Syria.288