Haka kuma Syriar ta zargi Turkiyya da kyale wasu 'yan bindiga dari suka shiga kasar Syriar.
Sai dai Firayim Ministan Turkiyya Ahmet Davutoglu ya ce kasarsa ta ta ci gaba da luguden boma-bomai a kan wuraren da Kurdawa suka kame a kan iyakar Turkiyya da Syria.
Turkiyyar ta bayana cewa kungiyar Kurdawa ta PYD na da alaka da mayakan sari-ka-noke na kungiyar PKK wadanda suka kwashe shekaru suna fada da gwamnatin Turkiyya.
Sai dai Amurka ta yi watsi da matsayin Turkiyya, tana kallon kungiyar PYD a matsayin kawar da za ta yi tasiri wajen yakar kungiyar IS a Syria.288