31 Janairu 2016 - 16:10
Sojojin Ruwa Na Iran Sun Gwada Sabbin Makaman Masu Linzami Da Suka Kera A Cikin Gida

Sojojin ruwa na kasar Iran sun gwada sabbin makama masu linzami da suka kera a cikin gida

Sojojin ruwa na kasar Iran sun gwada sabbin makaman linzami da sukakera a cikin gida a atisai na kwanaki hudu da suka kammala a yau Lahadi a wasu yankuna masu yawa a tekun farisa tekun inda da kuma mashigar ruwa ta Hurmuz.

Komandan sojojin ruwa kuma kakakin sojojin Sayyeed Mahmood Musawi kakakin ya fadawa yan jaridu cewa sun gwada makamai da dama a atisai na kwanaki hudu da suka kammala daga cikinsu akwai makaman linzami masu tafiya karkashin ruwa wadanda suka sami bararsu da aka sawwara ba tare da samun wata matsala ba.

Musawi ya kara da cewa sojojin nasa sun yi amfani da jirgin ruwa mai suna Jameran wajen cilla wadan nan makaman inzami, sanna sun yi amfani da juragen ruwa na submerin wanda atisayin.288