Kungiyar dai ta kai harin ne a sansanin sojin kenya da ke Somalia.
Janar Abas Ibrahim Gurey ya shaida wa BBC cewa an gabatarwa da rundunar sojin Kenya kwararan shaidu da ke nuna cewa al-Shabab da ke yankin Gedo na shirn kai musu hari.
Ya kara da cewa dakarun al-Shabab sun yi ta taruwa a yankin gabanin su kaddamar da harin.
Rundunar sojin Kenya dai ba ta ce komai a kan wannan batu ba.
Sai dai Shugaba Uhuru Kenyatta na Kenya yana halartar taron tunawa da sojojin kasar da aka kashe a harin na Somalia, a Nairobi, babban birnin kasar.
Kungiyar Al-Shabab ta ce ta kashe sojojin Kenya sama da 100 a lokacin da ta kai harin, ko da ya ke rundunar sojin Kenya ba ta tabbatar da yawan dakarunta da aka kashe ba.288