2 Janairu 2016 - 16:35
Iran Ta Jaddada Aniyarta Na Ci Gaba Da Fadada Karfin Makamanta Masu Linzami

Mataimakin babban kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran Birgediya Janar Husain Salami ya bayyana cewar Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba za ta dakatar da shirinta na kara karfafa makamanta masu linzami ba.

Janar Salami ya bayyana hakan ne a wani jawabi da yayi a jiya wajen sallar Juma'ar birnin Tehran inda yayin da yake mayar da martani da magangun jami'an Amurka kan makamai masu linzami na Iran din ya bayyana cewar: A yau jami'an Amurka suna maganar sake kakaba wa Iran takunkumi saboda batun fadada karfin makamanta masu linzami. Don haka muna sanar da Amurkawa cewa matukar dai kuka ci gaba da kashe al'ummar Palastinu, da Yemen da kuma sanya al'ummar Siriya zama 'yan gudun hijira, haka nan kuma matukar kuka ci gaba da kai hare-hare kan al'ummar Pakistan da kuma ci gaba da mamaye kasashen musulmi da kuma ci gaba da goyon bayan haramtacciyar kasar Isra'ila tana ruwan bama-bamai a kan al'ummar Labanon da Palastinu da Siriya, to kuwa za mu ci gaba da karfafa irin karfin makamai masu linzami da muke da shi.

Janar Salami ya kara da cewa a halin yanzu dai daruruwan rumbuna da ramukan karkashin kasa na dakarun kare juyin na Iran cike suke da nau'oi daban-daban na makamai masu linzami wadanda suke cikin shirin kare mutumci da 'yancin kasar Iran da kuma tabbatar da 'yancin musulman duniya, yana mai cewa koda wasa dakarun Iran ba za su kasa a gwiwa wajen kera makaman da suke bukata wajen kare kasar ba.

Kafin hakan ma dai shugaban kasar ta Iran Sheikh Hasan Ruhani ya ba wa ministan tsaron kasar umurnin ci gaba da kera makamai masu linzami na kasar ba tare da dakatawa ba a matsayin mayar da martani da matakin da Amurkan take dauka na sake kakabawa Iran din takunkumi wanda ya saba wa yarjejeniyar nukiliya da aka cimma tsakanin Iran da manyan kasashen duniya a kwanakin baya.288