Ma'aikatar harkokin cikin gida ta kasar Saudiyyah ce ta sanar da hakan a yau, inda ta tabbatar da cewa an kashe Sheikh Nimr Baqir Nimr jagoran mabya mazhabar shi'a a safiyar yau Asabar tare da wasu mutane 46.
Tun a cikin watan Yunin shekara ta 2012 ce masarautar Saudiyya ta kame Sheikh Nimr a yankin Qatif da ke gabacin Saudiyya, wanda akasarin mutanen yankunan lardunan gabacin kasar ta Saudiyya mabiya mazhabar shi'a ne, wadanda suke kokawa kan yadda gwamnatin kasar ta mayar da su saniyar ware a cikin dukkanin lamurra da suka shafi hakkokinsu na 'yan kasa, duk kuwa da cewa a yankunansu ne kasar take fitar da dukkanin danyen man fetur da isakar gas da ta dogara da shi.
Sheikh Nimr na daga cikin wadanda suke kira ga mahukuntan Saudiyya da su adalci wajen kula da 'yan kasa, maimakon mayar da wasu saniyar ware, wanda kuma hakan shi ne babban laifinsa wanda saboda hakan ne aka kame shi fiye da shekaru 3 da suka gabata, a yau kuma aka kashe shi.288