Dan kunar-bakin waken dai wanda yake a kan babur, ya daki kofar shiga wani ginin gwamnati a inda mutane suke a kan layukan karbar katin dan kasa suka rasu.
Wani wanda ya shaida yadda al'amarin ya faru, ya ce wurin da abin ya faru ya yi kaca-kaca da sassan jikin mutane da gilasai.
Wannan dai shi ne harin da yafi kowanne muni a shekarar 2015 bayan an samu tsaikon hare-hare.
Wani bangare na kungiyar Taliban mai suna, Jama'atul Ahrar ya dauki alhakin kai harin.288