A yau ne ake bukukuwan maulidin manzon Al...(s) da kuma jikansa mai tsari Imam Jaafar bin Mohammad Assadiq (a) a duk fadin Iran. Anan Tehran jagoran juyin juya halin musulunci AYa. Sayyeed Aliyul Khaminnaee. Ya gana da bakin da suka zo taron makon hadin kai karo na 29 da kuma jami'an diblomasiyya a husainiya na Imam Khomaini (q) da ke gidansa.
Jagoran ya kara da cewa lokaci yayi da musulmai zasu hada kai su kuma raya ci gaban da addinin musulunci yake da shi, don tuni rauni ya bayyana ga ci gaban da kasashen yamma suke ikrari.
Dangane da yadda musulmi suke shan wahala a kasashen duniya Aya. Sayyeed Aliyul Khami naee ya aza ayan tambaya kan yadda duniya ta yi shiri kan abin da yake faruwa da shugaban ya shia a Nigeria da mabiyansa da kuma kan yadda ake takuwa mutanen kasar Bahrain. Har'ila yau jagoran ya nuna takaicinsa kan yadda aka rusa kasashen Libya Syria da kuma Iraqi.288