Shugaban majalisar, Sanata Abubakar Bukola Saraki shi ne ya jagoranci zaman wanda aka amince da ministocin daya bayan daya.
Tun a ranar Talata majalisar dattawan ta tantance mutane 10 sannan kuma a ranar Laraba ta tantance mutane 8 inda jumlar ta zama mutane 18.
Majalisar dattawa ta jinkirta tantance tsohon gwamnan jihar Ribas, Rotimi Ameachi sai zuwa ranar Alhamis.
Matakin ya biyo bayan rashin mika rahoton kwamitin da'a da korafe-korafen jama'a na majalisar dattawan da ke binciken wani korafi a kan Mr Amaechi.
Shugaba Muhammadu Buhari ya aike wa majalisar sunayen mutane 37 ne domin ya nada su a matsayin ministoci kafin daga bisani ya janye sunan Alhaji Ahmed Ibeto daga jihar Niger.
Ga jerin wadanda aka amince da su:
- Sanata Udoma Udo Udoma daga jihar Akwa Ibom
- Kayode Fayemi daga jihar Ekiti
- Audu Ogbeh daga jihar Benue
- Ogbonayya Onu daga jihar Abia
- Osagie Ohanire daga jihar Edo
- Laftar Janar AbdulRahman Dambazau daga jihar Kano
- Alhaji Lai Muhammed daga jihar Kwara
- Hajiya Amina Mohammed daga jihar Gombe
- Injiniya Sulaiman Adamu daga jihar Jigawa
- Alhaji Ibrahim Usman Jibrin daga jihar Nasarawa
- Babatunde Raji Fashola daga jihar Lagos
- Ibe Kachukwu daga jihar Delta
- Alhaji Abubakar Malami daga jihar Kebbi
- Hajiya Aisha Alhassan daga jihar Taraba
- Solomon Dalong daga jihar Filato
- Chris Ngige daga jihar Anambra
- Hadi Sirika daga jihar Katsina
- Kemi Adeosun daga jihar Ogun