A gabashin birnin Kudus, an bayar da umarnin kafa wuraren binciken abubuwan hawa, ko da ya ke ba a kafa su a yankunan Palasdinawa ba, inda ake samun yawancin hare-haren.
An fara daukar matakin ne sakamakon amincewar da gwamnati ta yi ta bai wa 'yan sanda damar rufe wasu yankuna na gabashin birnin Kudus.
Kazalika, hukumomin na da damar rushe gidajen Falasdinawan da ke kai hare-hare a kan Yahudawa, sannan a hana su 'yancin ci gaba da zama a birnin Kudus.
An ci gaba da rikice-rikice a yankin ne sakamakon kwana da kwanakin da aka kwashe ana zaman zulumi a kan samun damar shiga Masallacin Al-Aqsa mai muhimmanci da Musulmai da Yahudawa. 289