4 Oktoba 2015 - 17:04
"Muna bincike kan hare-haren Abuja"

mutu sakamamRundunar sojin kasa ta Najeriya ta ce ta dukufa wajen bincike tare da shan alwashin kama duk wani mai hannu wajen kitsa hare-haren bama-bamai da aka kai Kuje da Nyanya da ke wajen birnin Abuja.

A hirar da ya yi da BBC, mai magana da yawun shedkwatar tsaron Nigeria Kanal Rabe Abubakar, ya ce rundunar ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen kawo karshen hare-haren kungiyar Boko Haram.

Kanal Rabe ya kuma ce"wadannan hare-hare da 'yan Boko Haram suka kawo ba za su girgiza mu ba ko kadan don duk alamu ne da ke nuna cewa karshensu ya zo."

Ya kara da cewa dukkan hukumomin tsaron Najeriya na aiki kafada da kafada wajen tattara bayanan sirri kan ayyukan da kungiyar ta Boko Haram ke gudanarwa.

A ranar Juma'a da daddare ne wasu 'yan kunar bakin wake suka kai hare-haren, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 18.