Mohammed Siddique mai shekaru 60, da dansa Mohammed Waqar mai shekaru 24 sun amsa laifin cin zalin yaro dan kasa da shekaru 16.
Sun buge yaron har sau hudu a masallacin Jamia na unguwar Sparkbrook da ke Birmingham a Ingila tsakanin watan Mayu zuwa Yunin 2014.
Mai shigar da kara na gwamnati, Sam Forsyth ya ce malaman Islamiyyar sun duke yaron da bulalar roba sannan kuma sun mare shi a cikin aji.
Malaman sun duke yaron sau hudu a lokuta daban-daban, kuma akwai hotunan da ke nuna shaidar bulala a kafarsa.
Lauyan da ke kare malaman, Charanjit Jutla ya ce malaman, mutanen kirki ne kuma sun yi nadamar abin da suka yi.
Sai dai alkalin kotun a Birmingham Mark Wall ya ce "ba za a laminci zalunci ba musamman bugu da sanda."289