8 Satumba 2015 - 17:36

Tun ba yau ba ne ake ta korafi game da batun rashin sanar da sunayen sabbin ministoci da shugaban kasar Nigeria Mohammad Buhari bai yi ba, wanan yasa shugaban ya bayyana a wani taro manema labarai tsakaninshi da shugaban ksar Ghana a wata ziyara da ya kai kasar ta Ghana, ind aya nuna cewa yana bin komai a hankali ne baya son yin gaggawa a zo ana da na sani , don haka idan har bai sanar da sunayen ministocin gwamnatin ba daga na zuwa karshen wata to a tuhume shi.

Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari, ya ce kafin karshen wannan wata na Satumba, zai bayyana sunayen ‘yan majalisar zartaswarsa kamar yadda ya yi alkawari a baya.

Wata sanarwa mai dauke da sa hanun mai bashi shawara kan yada labarai da hulda da jama’a, Femi Adesina, ta ce Buhari ya bayyana hakan ne yayin da ya ke jawabi a wani taron manema labarai na hadin gwiwa da shugaban Ghana John Dramani Mahama, a wata ziyarar aiki ta yini guda da ya kai Ghana.

“Bayan ranar 30 ga watan Satumba, ku tuhume ni idan ban nada ministoci na ba.” In ji Buhari, yayin da ya ke amsa tambaya kan dalilin da yasa bai nada ministocinsa ba.

Buhari har ila yau ya ce gwamnatinsa na yin galaba a kan ‘yan kungiyar Boko Haram tun bayan da ya kama mulki tare da taimakon dakarun hadin gwiwa na kasashen waje.

“Abin da na yi na farko shine a sake kintsa dakarun Nijeriya tare da basu umurni mara sarkakiya, kamar a fannin abinda ya shafi horaswa da samar musu da kayan aiki da kuma yadda aka rarraba su.” Inji Buhari.

Da farko, shugaban Ghana, Mahama ya ce sun tattauna da takwaransa na Nijeriya inda suka cimmam matsayi kan batutuwan da suka shafi huldar kasuwanci da samar da tsaro a yankunansu.288