29 Agusta 2015 - 18:20

wani jirgin saman mallakin sojojin saman Nigeria ya yi hatsari a yau a birnin Kaduna kuma ya yi sanadiyar mutuwar dukkan fasinjojin dake cikinsa, tunu kwamnadan hafsan sojin sama na Nigeria Sadiqu Abubakar ya isa inda hatsarin ya faru inda ya mika ta'aziya ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu, daga karshe ya nada kwamitin bincike kan musabbabin hatsarin.

Wani jirgin sojin saman Nigeria ya fadi a yau sakamakon hatsari da ya yi kuma ya yi sanadiyar mutuwar dukkan mutane dake cikinsa a birnin Kaduna .

Rahotanni sun bayyana cewa kakakin hukumar sojojin Sama ta Nigeria Dele Alonge ya bayyana cewa jiragiin saman na sojin saman Nigeria mai lambar NAF 030 yayi hatsari ne a barikin soji na Rubadu dake garin kaduna kuma babu wani daga cikin pasinja dake cikin jirgin da ya tsira da ransa, kuma ya zuwa yanzu ana ci gaba da gudanar da bincike domin tantance sunayen pasinjojin dake cikinsa da kuma gano musabbabin abin da ya jawo hatsarin.

Ana shi bangaren kwamandan Hafsoshin sama na Nigeria Air marshal Sadiq Abubakar ya kai ziyara a wajen da hatsarin ya faru tare da ganawa da iyalan wadanda suka rasa rayukansu , kuma ya kafa kwamiti da zai gudanar da bincike domin gano musabbabin hatsarin tare da mika sakamakon binciken cikin gaggawa288 .