|
Diyar marigayi Imam Khumaini ( RA) Ta girmama ‘yayan malam Guda 3 da suka yi shahada a lokacin muzahara Qudus a bara a Nigeria. A ci gaba da ziyarar da yake yi a Iran jagoran harkar musulunci a Nigeria Shaikh Ibrahim Zakzaki ya sami gagarumar tarba daga yar marigayi Imam khumaini wato Dr Zahra Mustafawy a lokacin taron da aka gudanar na girmama yayan malam guda guda 3 da suka yi shahada a lokacin muzaharar Qudus a shekarar bara, a Nigeria. Idan ana iya tunawa a shekara da ta gabata ce jami’an soji a Nigeria suka harbe yayan malam su 3 Ahmad, Hameed, da kuma Mahmud a lokacin muzaharar Qudus lamarin da ya jawo shahadarsu tare da wasu sama da 30, Daga karshe a lokacin taron an nuna wani faifan bidiyo na bangaren wannan waqiah da ta faru ta ranar Qudus wanda ya sanya da dama daga cikin mahalarta taron zubda hawaye |