Jami’an gwamnati sun ce jiya juma’a, ‘yan bindigan suka afka cikin Otel din da baki ke yawan zuwa, kuma kafin sojan su mayar da martani ‘yan bindiga suka yi garkuwa da mutanen dake wajen.
Wata majiya tace akwai ‘yan kasashen Afrika ta Kudu, Faransawa da dan kasar Ukraine a cikin Otel din lokacin da aka kai harin.
Kokarin dakarun kasar na tunkarar ‘yan bindigan ya sami koma baya, saboda kasancewar wadanda aka yi garkuwa dasu.
Wata sanarwar rundunar samar da zaman lafiyan Majalisar Dinkin Duniya ta MINUSMA a kasar, tace akwai jami’inta daya cikin wadanda suka rasa ransu a cikin gumurzun.288