Christon Scriven yace Dylann Roof din ya taba batun cewar zai kai hari a Jami'ar Charleston - to amma ya yi shiru a lokacinda aka yi masa tambayoyi.
A gurfanarsa ta farko gaban Kotu, 'yan uwan mutanen da aka kashe sun gaya ma Roof din dan shekaru 21 da haihuwa cikin halin da suka shiga, to amma wasunsu sun ce, sun gafarta masa.
Shugaba Obama ya yaba ma irin yadda mutane suka hada kai suna juyayin abinda ya faru, yana mai cewar dole ne a sake nazarin dokoki na mallakar bindiga.288