14 Yuni 2015 - 11:03
ICC ta bukaci Afirka ta Kudu da ta cafke El-Bashir

Kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ICC ta bukaci hukumomin kasar Afirka ta kudu da su kama shugaban Sudan Umar Hasan El-bashir wanda ke halarar taron shugabannin Afirka yanzu haka a birnin Johannesburg

A wani sako da ya fitar a wannan lahadi, Shugaban Kotun ta duniya Sidiki Kaba, ya ce alhaki ya rataya a wuyan hukumomin kasar ta Afirka ta kudu da su cafke El-Bashir sannan kuma su tusa keyarsa zuwa birnin Hague domin ya fuskanci shari’a dangane da laifufukan yaki da na cin zarafin bil’adama da ake zargin sa da aikatawa a Darfur.

Tun shekara ta 2009 ne dai kotun ta fitar da sammanci kasa da kasa domin a kama shugaban na Sudan, lamarin da ya sa ya taikata tafiye-tafiyensa zuwa wasu kasashen duniya.288