Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{a.s}-abna-a sakamakon harin da wasu mahara suka kai ma wasu 'yan shi'a ranar lahadi yayi sanadiyar shahadar mutane biyar.
'yan sanda yankin Balujistan sun bayyana cewa, maharan sun zone kan Babura kuma ba wanda ya sheda ko su wanene bayan sun bude wuta akan mutanen dake tsaye bakin wani gidan cin abinci ,kuma suka guda daga wurin. Wani jami'an 'yan sandan yace da alama harin an shirya sa ne.
Kama yanzu ba wani mutun ko kungiya wanda ya dauki alhakin kai harin, sai dai ana zargin kungiyar 'yan ta'addannan wato saifa sahaba da kai harin.
Firaministan Pakistam Muhammad Nawaz Sharif yayi Allah wadai da kai harin , inda ya bugaci gaggauta binciko maharani domin a hukunta su. ABNA 288