8 Yuni 2015 - 10:41
Sojin Iraki sun 'yanto garin Biji.

Rundunar sojin Iraki tare da hadin gwiwar sojojin sa kai sunyi nasarar 'yanto garin Biji baya kwashe sati biyu ana dauki ba dadi da 'yan ta'addan Da'ish.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{a.s}-abna-ya rawaito shugaban rundunar Ahlilhak shaikh kais khaz Ali na cewa, mun 'yanta garin Bijin daga 'yan ta'adda.

Ya kara da cewa, mun dora tutar Iraki sama gine gine na kwamnati.

Shugaban rundunar ya kara da cewa, hadin gwiwa tsakanin sojoji da rundunar mayakan sa kai da kuma taimakon jiragen yakin sama yasa muka samu nasarar 'yanta garin, kuma 'yan ta'adda da dama ne suka rasa rayukan su sannan sukayi hasarar kayan yaki da yawa.ABNA .288