7 Yuni 2015 - 10:05
An yi zana'idar Ayatullah Asifi a garin Najaf Iraki.

Zana'idar Ayatullah Asifi wakilin jagoran juyin musulunci na Iran a Iraki ta samu halarta manyan maluma da kuma Firaministan kasar.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{a.s}-abna-ya rawaito cewa, an gudanar da zana'idar babban malami mai tsoran Allah Ayatullah Asifi a ranar lahadin jiya a Haramin Imam Ali{a.s}, zana'idar ta samu hallarar mutane da dama daga ciki akwai manyan maluman da maraja'an takalidi da kuma Firaministan kasar wato Haidar Abadi da sauran manyan mutane na kasar ta Iraki.

Kafin cikawar sa Ayatullahi Asifi shine wakilin jagoran juyin musulunci na Iran a Kasar Irakin kuma babban jigo a cibiyar Ahlul-Baiti{a.s} a Duniya, Allah ya gafarta masa Ameen.Abna 288

288