Sai dai kuma bangaren Ansarullah na Houthi, Yemen dake rike da mafi yawancin kasar sunki halartan wannan taro.
Taron na zuwa ne yau lahadi, rana ta karshe cikin kwanaki biyar na tsagaita wuta domin kai kayan agaji ga mabukata dake Yemen.
Tsohon Shugaban Yemen Abd-Rabbu Mansour Hadi dake gudun hijira zai yi jawabi a taron na yau.
Bayanai na nuna duk da tsagaita wuta da akayi anyi ta samun hare-hare a wasu sassan kasar ta Yemen.ABNA