Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa na Ahlul Bayt As – ABNA - ya habarta cewa: rundunar sojin kasar Yemen ta sanar da aiwatar da ayyukan soji a filin tashi da saukar jiragen sama na Ramon da kuma wani muhimmin wuri na mamayar da haramtacciyar kasar Isra'ila ta mamaye a kasar Falasdinu.
Kakakin rundunar sojin kasar Birgediya Janar Yahya Saree ya tabbatar da cewa rundunar sojin saman ta kai farmakin soji guda biyu. Na farko dai ya auna filin jirgin saman Ramon na makiya Isra'ila da ke yankin Ummur-Rashrash a kudancin kasar Falasdinu, inda suka yi amfani da jirage marasa matuka biyu.
Saree ya kuma bayyana cewa, an kai farmakin na biyu ne kan wani muhimmin waje da makiya yahudawan sahyoniya a yankin Jaffa da suka mamaye ta hanyar amfani da wani jirgi mara matuki na "Jaffa".
A halin da ake ciki kuma, sanarwar da rundunar sojin Yaman ta fitar ta bayyana cewa, hare-haren sun hada da harin da aka kai kan jirgin ruwan Amurka Truman da wasu jiragen yakinsa a arewacin tekun Bahar Maliya, ta hanyar amfani da makami mai linzami da jirage marasa matuka.
A cikin wannan yanayi, Birgediya Janar Saree ya tabbatar da cewa, wannan farmakin ya zo ne a matsayin mayar da martani ga hare-haren wuce gona da iri da Amurka ke kaiwa kasar Yemen da laifukan da take aikatawa kan al'ummar kasar Yemen.
Ya yi nuni da cewa, wannan aiki mai inganci ya haifar da wargaza wani hari ta sama da makiya Amurka ke shirin aiwatarwa, da kuma fadowar wani jirgin sama samfurin F-18 na Amurka sakamakon yanayin rudani da firgici da ya mamaye sahun makiya a yayin harin.
Ya kuma yi nuni da cewa harin ya kai ga jirgin dakon kaya na Amurka Truman ya tsere zuwa arewa mai nisa da tekun Bahar Maliya.
Ya kara da cewa, an kai harin ne kafin makiya Amurka su sanar da dakatar da kai farmakin da suke kai wa Yemen.
Birgediya Janar Saree ya jaddada cewa sojojin kasar Yemen "ba za su yi kasa a gwiwa ba wajen kai munanan hare-hare kan makiya Amurka idan suka dawo da kai farmaki kan kasarmu," yana mai tabbatar da cewa "ayyukanmu za su ci gaba da kai hare-hare har sai an daina kai hare-hare a zirin Gaza tare da kawar kewayewar da akaiwa Gaza.
Ya yi nuni da cewa al'ummar kasar Yemen sun tsaya tsayin daka wajen tabbatar da adalci, suna fafutukar neman yardar Allah, kuma suna aiwatar da ayyukansu na addini, da dabi'u, da kuma jin kai ga al'ummar Palastinu da ake zalunta da dukkanin al'ummomin kasashen Larabawa da na Musulunci, da kin mika wuya da takura, kuma ba za su ja da baya ba, kuma ba za su mika wuya ba, ba tare da la'akari da abin da zai biyo baya ba.
Da yake karkare jawabinsa, kakakin rundunar sojin kasar Yemen ya tabbatar wa al'ummar kasar Yemen cewa "dakarun sojin kasar sun mallaki karfin soji da ke ba su damar mayar da martani mai kyau kan harin da Isra'ila ke kai wa".
Your Comment