Kamfanin Dillancin labaran ƙasa da ƙasa na Ahl-Bait As -Abna- ya habarta Yahya Saree, kakakin rundunar sojin Yaman:
Mun gudanar da hare-haren soji guda biyu a kan jiragen dakon kaya Truman da Vinson da dakarunsu a cikin Tekun bahri maliya da na Arab, kuma wannan shi ne karo na farko da aka kai wa Vinson hari tun bayan shigarsa Tekun Arabiya.
Sojojin saman mu sun yi nasarar harbo wani jirgin yakin Amurka mara matuki kirar MQ-9 a lokacin da yake gudanar da ayyukan leken asiri a sararin samaniyar lardin Sana'a.
Ya kara da cewa: Rukunin makami mai linzamin mu sun kai hari da makami mai linzami na "Zolfaghar" a kusa da filin jirgin sama na Ben-Gurion da ke yankin Yafa da yan mamaya suka mamaye.
Your Comment