9 Afirilu 2025 - 13:57
Source: ABNA24
Fiye Da Shahidai 70 Da Kuma Jikkatar Da Dama A Sabon Harin Da Isra’ila Ta Kai A Gaza

Harin bam da aka kai sama da wurare 45 a Gaza cikin sa'o'i 24 da suka gabata zuwa yanzu Adadin gab ki dayan shahidai a harin da Isra’ila ke kaiwa Gaza ya karu zuwa 50,846.

Kakakin rundunar sojin Isra'ila ya sanar da cewa, jiragen yakin gwamnatin kasar sun yi ruwan bama-bamai fiye da 45 a yankuna daban-daban na zirin Gaza a cikin sa'o'i 24 da suka gabata.

Shahidai uku da wasu da dama sun jikkata a harin bam na Gaza

Jiragen yakin haramtacciyar kasar Isra'ila sun yi ruwan bama-bamai a wani gida da ke kusa da masallacin Al-Hawashi da ke unguwar Shuja'iya a birnin Gaza. Falasdinawa uku ne suka yi shahada yayin da wasu da dama suka jikkata sakamakon wannan aika-aika.

Mutane 40 ne suka yi shahada tare da jikkata sakamakon wani sabon laifin yahudawan sahyuniya a yankin Shujaiyeh na Gaza

Akalla mutane 5 ne suka mutu sannan wasu fiye da 35 suka jikkata sakamakon wani harin bam da Isra'ila ta kai kan wani gini da ke kusa da wani masallaci a unguwar Al-Shuja'iya da ke gabashin birnin Gaza.

A wani harin ta’addancin na kisan kiyashi da Isra’ila ta aikata na baya-bayan nan cikin awa 24, sojojin haramtacciyar kasar Isra'ila sun yi ruwan bama-bamai a unguwar Shujaiyeh da ke gabashin birnin Gaza.

Majiyoyin kiwon lafiya sun sanar da cewa Palasdinawa 20 ne suka yi shahada yayin da wasu 50 kuma suka jikkata sakamakon wannan aika-aika.  Yawan shahidan wannan laifi na iya karuwa a kowane lokaci.

Ma'aikatar lafiya ta kasar ta sanar da cewa tun bayan barkewar yakin da kuma hare-haren da makiya yahudawan sahyoniya suka kai a zirin Gaza a ranar 18 ga watan Maris, Palasdinawa 1,482 ne suka yi shahada yayin da mutane 3,688 suka jikkata.

Haka kuma, adadin shahidan yakin tun ranar 7 ga Oktoba, 2023 ya karu zuwa 50,846, kuma adadin wadanda suka jikkata ya karu zuwa 115,729.

Your Comment

You are replying to: .
captcha