Yanayin farin ciki ya bace ɓat daga rayuwar al'ummar Gaza, an share murmushi daga fuskokinsu saboda hare-haren Isra'ila. A shekara ta biyu a jere, yaran Gaza na gudanar da bukukuwan Sallar Idi a cikin baraguzan gidaje da tantuna, sakamakon ci gaba da kai farmakin da Isra'ila ke yi a yankin, suna cikin mawuyacin hali na rashin tausayi da jin kai.

Wannan bidiyon wata hira ce da gidan talabijin na Aljazira suka yi da waɗansu yara da ke Rayuwa cikin tantuna da baraguzan gidaje a lokacin sallah Idi na bana 2025
Your Comment