22 Maris 2025 - 10:43
Shekaru 21 Da Shahadar Sheikh Ahmed Yassin

A yau Asabar ne ake cika shekaru 21 da shahadar jagoran gwagwarmayar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas Sheikh Ahmed Yassin wanda jiragen yakin haramtacciyar kasar Isra'ila suka kashe bayan ya gabatar da sallar asubahi.

A yau Asabar ne ake cika shekaru 21 da shahadar jagoran gwagwarmayar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas Sheikh Ahmed Yassin wanda jiragen yakin haramtacciyar kasar Isra'ila suka kashe bayan ya gabatar da sallar asubahi.

A cewar cibiyar yada labaran Falasdinu, kisan nasa yazo a wani muhimmin lokaci ne da ya dauki hankulan duk masu neman 'yanci a duniya tare da fadakar da al'ummar Larabawa da na Musulunci hakikanin hatsarin da mamayar Isra'ila ke da shi ga kasar Falasdinu.

Tun a shekarun 1960 ne sunan Sheikh Ahmed Yassin ke da alaka da manufar gwagwarmaya da kira gare ta, ta yadda ya jaddada hakan a dukkan matsayi da tunaninsa. Ya zama "uba na ruhaniya" na ra'ayin gwagwarmaya a aikace, tun kafin a aiwatar da ra'ayinsa ta hanyar yunkurinsa.

Sheikh Yassin ya kasance wani babban mai matsayi na ruhi da siyasa a tsakanin al'ummar Palastinu da gwagwarmaya, ta yadda siffarsa ta kasance a cikin zukatan mutane a matsayin daya daga cikin muhimman alamomin tarihi da gwagwarmaya a Palastinu a karnin da ya gabata.

Ya zaburar da matasan Falasdinawa masu kishin ‘yanci da ‘yantar da su daga mamaya, da su ci gaba da bin tafarkinsa na jihadi, da gwagwarmaya, da ‘yancin da ya tsara da jininsa.

A safiyar ranar 22 ga watan Maris din shekarar 2004 ne jiragen yakin haramtacciyar kasar Isra'ila suka kai masa hari a kan hanyarsa ta dawowa daga sallar asuba, lamarin da ya yi sanadin shahadar Sheikh Yasin tare da wasu mutane bakwai.

Wannan safiya mai cike da bakin ciki ta kawo karshen wata tafiya Mai girma inda ya gabatarwa duniya ɗaya daga cikin masu fada a ji a fagen gwagwarmaya wajen fuskantar Yan mamaya, inda ya bar gadon baya na gwagwarmaya da ruhin jihadi mai rai a tsakanin al'ummar Palastinu da kuma nuna adawa da zalunci da ayyukan mamaya.

Haihuwa Da Kafa Harkar Gwagwarmaya Ta Hamas

An haifi Sheikh Yassin a shekarar 1936 a kauyen "Al-Jura" da ke yankin Ashkelon. Amma a shekara ta 1948 kungiyoyin yahudawan sahyoniya sun tilastawa iyalansa tare da dubban daruruwan Falasdinawa yin hijira zuwa zirin Gaza.

Yana da shekaru 16, a cikin watan Yuli 1952, wani mummunan al'amari ya faru da shi. Yayin da yake aikin motsa jiki a bakin teku, ya yi hatsari da ya sa ya shanyewar jikinsa gabaki ɗaya.

Ya yi aiki a matsayin malamin Larabci da ilimin addini, kuma a lokaci guda ya kasance mai yin wa'azi da bayani a masallatan Gaza. Wa’azozinsa sun yi suna sosai saboda karfin hujjoji da jajircewa wajen bayyana gaskiya. Haka nan kuma ya jagoranci ‘yan uwa musulmi a Gaza kuma ya taka rawar gani wajen gudanar da ayyukan da’awah da zamantakewa.

Bayan mamayar Falasdinu a shekara ta 1967, ayyukan zamantakewa da tabiligi na Sheikh Yassin sun fadada, kuma ya kafa dandalin Musulunci, wanda ya zama daya daga cikin muhimman cibiyoyi na ayyukan Islama a zirin Gaza.

A shekarar 1983, gwamnatin Sahayoniya ta kama shi bisa zargin "mallakar makamai, kafa kungiyar soji, da kuma ruguza Isra'ila". Wata kotun soji ta Isra'ila ta yanke masa hukuncin daurin shekaru 13 a gidan yari, amma an sake shi a shekara ta 1985 a matsayin wani bangare na yarjejeniyar musayar fursunoni tsakanin gwamnatin sahyoniyawa da kungiyar Popular Front for the Liberation of Palestine.

A watan Disambar 1987, Sheikh Yassin tare da gungun masu fafutukar Musulunci, suka kafa kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas a Gaza. Daga nan ne gwamnatin mamaya ta yi masa barazanar korar shi, kuma a watan Agustan shekarar 1988 sojojin yahudawan sahyoniya suka yi bincike a gidansa tare da yi masa barazanar korarsa zuwa kasar Labanon.

Bibiyarsa Da Kama Shi 

A ranar 18 ga watan Mayun shekarar 1989 ne gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila ta kame Sheikh Yassin tare da daruruwan 'yan kungiyar Hamas don hana yaduwar gwagwarmayar makamai, wanda a lokacin ya hada da hare-hare da wukake kan sojojin Isra'ila da matsugunan Isra'ila.

A ranar 16 ga Oktoba, 1991, wata kotun sojan Isra'ila ta yanke masa hukuncin daurin rai da rai tare da shekaru 15 bisa zargin kafa kungiyar Hamas, da kafa reshen soja na kungiyar (Izzuddin Qassam), da kuma tunzura sacewa da kashe sojojin Isra'ila.

Amma a ranar 1 ga Oktoba, 1997, an saki Sheikh Yassin sakamakon yarjejeniya tsakanin Jordan da Isra'ila. An yi wannan yarjejeniya ne domin sakin wasu jami’an leken asirin Mossad guda biyu wadanda ke da hannu wajen kashe tsohon shugaban ofishin siyasa na Hamas Khaled Meshaal da bai yi nasara ba.

Bayan da aka sake shi, ya fara sake gina ginshikin Hamas, musamman bayan da jami'an tsaron PA, karkashin matsin lamba daga Isra'ila, suka yi yunkurin wargaza kungiyar.

Hukumar Falasdinawa ta sanya shi zaman killace na tilas a lokuta biyu, a cikin Disamba 2001 da Yuni 2002. Duk da wannan gazawar, Sheikh Yassin ya jaddada hadin kan kasa tare da dagewa kan hadin kan al'ummar Palastinu.

A watan Mayun 1998, ya tafi balaguron waje don samun tallafin kuɗi da Ruhiyya ga Hamas. Tafiyar ta fusata Isra'ila kuma ta sa Mossad ta dauki matakan tsaro da dama don hana "hazgunawa Isra'ila a waje".

Jihadi Da Gwagwarmaya 

Sheikh Yassin ya kasance yana jaddada hadin kan kasa tare da daukarsa a matsayin daya daga cikin tushen gwagwarmayarsa. Ya kuma ba da muhimmanci musamman kan batun fursunonin Palastinawa, ya kuma jaddada cewa, ya kamata a yi duk mai yiwuwa wajen ganin an kubutar da su. Shahararriyar maganarsa, "Dole ne mu 'yantar da 'ya'yanmu, ko da ta hanyar tilasta musu sakinsu ne don dole," har yanzu wannan burin yana raye a cikin kwakwalan Falasdinawa.

Ya goyi bayan aiwatar da ayyukan hadin gwiwa tsakanin dakarun Qassam da sauran kungiyoyin gwagwarmaya tare da jaddada bukatar dukkanin kungiyoyi su hada kai don yakar abokan gaba.

Daga karshe Sheikh Yassin ya yi shahada bayan kammala sallar asuba a ranar 22 ga Maris, 2004, inda ya bar abin koyi na gwagwarmaya da gwagwarmaya ga al'ummar Palastinu. Shahadarsa ta haifar da fushin jama'a da zanga-zanga a duniya.

Bayan kashe Sheikh Yassin, kungiyar Hamas ta shiga zaben 'yan majalisar dokokin kasar a shekara ta 2006, tare da samun gagarumar nasara ta kafa gwamnatin Falasdinu.

Yanzu haka dai a zagayowar ranar shahadar Sheikh Yasin, al'ummar Palastinu na ci gaba da fuskantar kisan kiyashi da zaluncin gwamnatin sahyoniyawan da suke yi a zirin Gaza. Tun daga ranar 7 ga Oktoba, 2023, wannan mummunan yakin ya yi sanadin shahidai fiye da mutane 162,000 da jikkata, wadanda yawancinsu mata da yara ne. Haka kuma, sama da mutane 14,000 ne suka bace a karkashin baraguzan ginin.

Cibiyar Sadarwar Falasdinu

https://farsi.palinfo.com

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha