20 Faburairu 2025 - 17:15
Bidiyoyin Yadda Hamas Ta Miƙa Gawarwakin Fursunonin Isra'ila 4

A Yau Alhamis Hamas ta bayar da gawarwarkin yahudawan sahyoniya 4 ga kungiyar agaji ta Red Cross

Ƙungiyar Hamas ta mika gawarwakin fursunonin yahudawan sahyoniya hudu ga dakarun Red Cross a Khan Yunis da ke kudancin zirin Gaza.

Wadannan fursunoni dai an kashe su ne sakamakon harin bam da sojojin haramtacciyar kasar Isra'ila suka kai a lokacin mamayar Gaza, kuma wata babbar tutar da kungiyar Hamas ta dora a wurin taron tana nuni da Netanyahu da sojojinsa a matsayin suke da alhakin mutuwarsu kuma sune wadanda suka kashe fursunonin sahyoniyawan.