29 Disamba 2024 - 13:16
An Gabatar Da Taron Tunawa Da Iyayen Annabi Muhammad (Sawa) A Katsina + Hotuna

A ranar Laraba 25/12/2024 ne ’Yan’uwa Musulmi almajiran Sayyid Zakzaky (H) na Da’irar Katsina suka gudanar da taron tunawa da Mahaifan Manzon Allah (Sayyid Abdullahi da Sayyida Amina A.S).

Taron wanda shi ne karo na farko da aka fara gudanawar a Da’irar, kuma aka yi masa laƙabi da ‘RANAR IYAYE TA DUNIYA’ wato ranar ce tafi dacewa da ranar Mauludin Mahaifan Annabi Muhammad (S.A.W.W). Wannan taro dai wasu ba’adin Matasan mawaƙa ne na ‘Fiyayyar Mata Group’ suka ɗauki nauyinsa, kuma suka shirya.

Da farko dai Sayyid Badamasi Yaqoub na cikin manyan baƙin da suka halarci taron kuma ya gabatar da jawabi na farko, sannan Shaikh Yakub Yahya Katsina ya gabatar da jawabinsa daga ƙarshe. A jawabin na Sayyid Badamasi ya fara da taya ’yan’uwa gami da Shaikh Yakub ta’aziyya na rashin da suka yi na Malama Binta. Ya kuma bayyana farin cikinsa matuƙa da wannan tunani da ’yan’uwan da suka yi na raya wannan munasaba.

A jawabin nasa ya nuna cewa tun daga Annabi Adamu (A.S) har zuwa kan Abdullahi (A.S) babu mushiriki ko ɗaya a Nasabar Annabi (S), kamar yadda ayar ƙur’ani ta nuna cewa: وَتَقَلُّبَكَ فِي السَّاجِدِينَ... Ma'ana yadda hasken Manzon Allah (S) ya riƙa ciratuwa zuwa tsatso daban-daban har ya iso kan Sayyid Abdullahi (A.S).

Shi kuwa a jawabin Shaikh Yakub Yahya ya fara ne da karanto Nasabar Annabi (S) da kuma Hadisai da suke tabbatar da Imanin Sayyid Abdullahi da Sayyida Amina, ba kamar yadda wasu suke ɗauka cewa wai ba Musulmi ne ba... Haka kuma ya faɗakara da ’ya'ya kan biyayya ga iyaye duba da alaƙanta ranar da ranar Iyaye, da kuma nauyin ’ya’ya a kan iyayen suma.

Tun da farko dai sai da Shaikh Yakub ya bayyana cewa: An fitar da ranar ne domin a haɗe ta cikin murnar Mauludin Sayyida Zahra (A.S) wanda shi ma cikin ranakun ne ya gudana. Ya ƙara da cewa: Wannan ba sabon abu ne ba na haɗe munasabobi duba da a ranar Haihuwar Manzon Allah (S) ita ma ana haɗa ta da Mauludin Jikansa Imam Jafaru Sadiq (A.S) da kuma ranar Mauludin Imam Khomaini (Q.S) da ya dace da ranar Mauludin Sayyida Zahra (A.S).

Bayan Kammala jawaban nasu, sai aka yanka alkaki da kuma raba kyautuka, inda aka karrama mahaifan Sayyid Zakzaky (H) a matsayinsu na iyayen wannan harka, da kuma mahaufana Shaikh Yakub Yahya Katsina.

Duka taron ya gudana ne a Muhallin Markaz Katsina da yammacin ranar ta laraba, kuma cincinrandon ’yan’uwa ne suka halarta da Sha’irai na ɓangarori daban-daban na Ɗariƙu inda da dare aka gabatar da Majalisin mawaƙa.

28Dec2024

@ShaikhYakubYahyaKatsina