10 Disamba 2024 - 16:29
Tawagar Kungiyar Tahrir Sham Ta Ziyarci Haramin Sayyida Ruqiyyah (AS) + Bidiyo

Tawagar kungiyar Tahrir Sham ta ziyarci hubbaren Sayyida Ruqiya (AS) da ke birnin Damascus.

Kamfanin dillancin labaran ƙasa da ƙasa na Ahl-Bait As ABNA ya habarta cewa: Haramin Ruqyah (a.s) ya fitar da wata sanarwa inda ya bayyana ziyarar da wata tawaga daga kungiyar Tahrir Sham ta kai wannan wuri mai alfarma a birnin Damascus.

Ya zo a cikin wannan bayani cewa: Muna sanar da ma'abota ibada a haramin Sayyida Ruqiya, tsira da amincin Allah su tabbata a gare ta, cewa wata tawaga daga kungiyar Tahrir Sham ta ziyarci haramin tare da mutunta ladubba da dabi'u na Musulunci sannan sun bar haramin bayan awa daya.

Ya kamata a lura da cewa, a yayin da ake gudanar da sauye-sauyen gwamnati a kasar Sham tare da karbe ikon kasar da kungiyar Tahrir Sham ta yi, babu wani kutsa kai cikin haramin Sayyida Ruqiyyah (a.s) kuma wannan harami mai tsarki yana cikin cikakken tsaro da ke cibiyar birnin Damascus.