10 Disamba 2024 - 12:53
Bayanin Shugaban Majalisar Malamai Na Mazhabar Ahlul-Baiti Ta Kasar Siriya Bayan Kifar Da Gwamnatin Bashar Assad/

Rayuka Da Dukiyoyi Da Wurare Masu Tsarki Na 'Yan Shi'ar Siriya Na Cikin Aminci.

A cikin wata sanarwa da shugaban majalisar malamai na mazhabar Ahlul-baiti ta kasar Siriya ya yi jawabi ga 'yan shi'ar kasar ya ce a bisa alkawarin 'yan'uwanku muminai, rayukanku da dukiyoyinku da wuraren ibada masu tsarki da sauran al'amuran addini su na cikin aminci.

Kamfanin dillancin labaran ƙasa da ƙasa na Ahl-Bait As ABNA ya habarta cewa: Hujjatul-Islam wal Muslimeen, Sayyid Abdullah Nizam shugaban majalisar malamai na mazhabar Ahlul-baiti (A.S.) Kasar Syria kuma dan kasar Syria mamba a majalisar Ahlul-baiti (A.S) ta duniya, bayan abubuwan da suke faruwa a kasar Syria da kuma faduwar gwamnatin Bashar Assad ya fitar da sanarwa.

A cikin wata sanarwa da shugaban majalisar malamai na mazhabar Ahlul-baiti ta kasar Siriya ya yi jawabi ga 'yan shi'ar kasar ya ce a bisa alkawarin 'yan'uwanku muminai, rayukanku da dukiyoyinku da wuraren ibada masu tsarki da sauran al'amuran addini su na cikin aminci.

Cikakken fassarar hausar wannan bayani da aka fitar a cikin harshen Larabci shine kamar haka;

بسم الله الرحمن الرحیم

الحمدالله رب العالمین و الصلاه و السلام علی سیدنا محمد و علی آله و صحبه و من تبعه باحسان الی یوم الدین

Da Sunan Allah, Mai Rahama Mai Jinkai

Godiya ta tabbata ga Ubangijin talikai, tsira da amincin Allah su tabbata ga Sayyidna Muhammad da alayensa da sahabbansa, da wadanda suka bi tafarkinsa da kyautatawa har zuwa ranar Alqiyama.

Ya ku ‘yan uwa muminai mabiya mazhabar ahlulbaiti na kasar Siriya, kun san irin wahalhalun da al’ummarmu suka shiga sakamakon rikice-rikice na cikin gida da fasadi da gazawar gwamnati da kuma yake-yaken da suka biyo baya, kuma kamar sauran kungiyoyi al’ummar Siriya kun sha wahala daga wadannan abubuwan da suke faruwa a yanzu da izinin Allah an samu sauyi a kasar Siriya, kuma ina rokon Allah Madaukakin Sarki da ya sanya kasar Siriya a cikin mafi kyawun yanayinta da wannan sauyi.

Ya ku ‘yan uwa, rayuwarku, dukiyoyinku, wurare masu tsarki da sauran al’amuran addini suna cikin aminci bisa ga alkawarin ’yan’uwanku masu aminci. Hakki ne da ya rataya a wuyan ’yan’uwanku a Musulunci ku zauna lafiya a gidajenku. Kun zauna tare da ’yan’uwanku na ɗaruruwan shekaru a ƙasarku kuma kuna tare da su a cikin baƙin ciki da farin ciki, kuma kun bar tasiri mai kyau a Siriya. In sha Allahu 'yan'uwanku za su yi riko da alqawarin da suka yi, kuma in sha Allahu babu wata cuta da za ta same ku matuqar kun dage da rayuwa cikin kwanciyar hankali da kyakkyawar niyya wajen ci gaban qasar mu, don haka ku ci gaba da wannan halayya kuma kar kuyi sabaninta kuma duk wanda ya keta wannan dabia’a alhakin yana kansa kuma ba mu da alhakin aikinsa.

Ina godiya ga ’yan’uwan da suka yi alkawarin ba da kariya ga bangarori daban-daban na al’ummar kasarmu ta Siriya tare da ba su tabbacin a kan haka. Allah ya ba wa wadanda suke da gaske wajen neman daukaka, kwanciyar hankali da adalci a kasar nan.

Muna rokon Allah Madaukakin Sarki da Ya kare kasarmu daga dukkan sharri, Ya kuma bai wa daukacin al’ummarta lafiya da karfin warkar da raunukan da da aka samu.

Shugaban Majalisar Malamai na Mazhabar Ahlul Baiti ta Siriya

Sayyid Abdullahi Nizam

Yana da kyau a lura cewa, bayan isar da wasu kungiyoyi masu dauke da makamai masu adawa da gwamnatin Syria zuwa Damascus, babban birnin kasar Syria, a ranar Lahadi 8 ga watan Disamba, 2024, an cire shugaban kasar Bashar Assad daga karagar mulki a hukumance, kuma Shugabancinsa a kasar Syria ya kare bayan shekaru 24.