Gidan talabijin na
Al-Mayadeen ya ruwaito cewa, Isra'ila ta
matsa da tankunanta zuwa nisan kilomita 20 daga Damascus bayan ta mamaye
kauyukan da ke kudancin babban birnin kasar Siriya.
Sojojin Isra'ila sun kuma kwace yankin da ke kusa da tuddan Golan da aka mamaye. A hakan tana mai karya yarjejeniyar rabewa ta 1974.
Bugu da kari, Isra'ila ta karbe iko da tsauni mai muhimmanci na Harmon, inda ta tabbatar da amincin tudu a yankin. Manyan kasashen yankin da suka hada da Iran da Jordan da Saudiyya sun yi Allah wadai da wannan ta'asa. Wanda suke ɗauki hakan a matsayin keta dokokin kasa da kasa da ke da nufin tada zaune tsaye a Syria. Hare-haren da Isra'ila ke kai wa a Syria ya tsananta, inda aka samu rahoton kai samame kusan 300 a cikin kwanaki biyun da suka gabata.
Wadannan hare-haren na nufin raunana Syria ne ta fannin soji, tare da barin ta cikin rauni da rashin tsaro. Wani abin mamaki har yanzu HTS da Turkiyya ba su mayar da martani kan mamayar da Isra'ila ke yi a Siriya ba.
Ya zuwa yanzu dai gwamnatin mamaya ta mamaye kauyuka da dama da ke wajen birnin Damascus.
Wannan ba shine kadai shirin Isra’ila ba akan Siriya haramtacciyar gwamnatin Isra’ila na ci gaba da kai hari da bama-bamai zuwa kasar ta Siriya. A wanin salon kuma tare kashe manyan masana da manyan malaman kasar ta Siriya domin a wani hari da take kaiwa na dauki daidai in da aka kashe Dr. Hamdi Ismail Nadi, masanin kimiyyar sinadarai, a gidansa da ke Damascus.
Wasu mutane da ba a san ko su waye ba ne suka kashe Dr. Hamdi Ismail Nadi, wani fitaccen masanin kimiyyar sinadarai a cikin gidansa da ke Damascus.
Wannan lamarin ya haifar da damuwa game da maimaita irin wannan yanayin a Iraki da kuma kai hari ga masana kimiyya da manyan masana kimiyya.
Sannan an kara samun aiwatar da kisan wani malamin addini a Damascus inda Majiyoyin yada labarai na Syria sun rawaito cewa wasu da ba a san ko su waye ba sun kashe Sheikh Tawfiq al-Bouti dan Sheikh Mohammad Saeed Ramadan a Damascus.