Shafin yada labaran yahudawan sahyoniya "Wallah" ya bayar da rahoton tuntubar juna kai tsaye da kuma ta hanyar masu shiga tsakani da kungiyoyi da dama a kasar Siriya, ciki har da kungiyar 'Hayat Tahrir al-Sham' (tsohuwar kungiyar Al-Nusra) da ke dauke da makamai bayan mamayar da suke a Siriya.
Wannan sansanin ya kara da cewa: A wannan mataki, Isra'ila na son kada masu dauke da makamai su tunkari kan iyaka (Syria da yankunan da ta mamaye).
Bidiyon Yadda Mutane Suka Shiga Gidan Bashar Assad Da Wawashe Kayan Da Ke Ciki
Duk da cewa Jolani ya ba da umarnin kada a kai hari kan kadarorin jama'a da na gwamnati, wasu 'yan adawa sun shiga gidan Bashar Assad da ke Damascus suka yi awon gaba da kayayyakin da ke ciki.
