Kamfanin dillancin labarai kasa
da kasa na Ahlul-Baiti (A.S) ABNA ya habarta maku cewa, mayakan kungiyar
takfiriyya ta Tahrir Sham sun shiga birnin Hama da ke tsakiyar kasar Siriya.
'Yan ta'addan sun shiga ne daga yankin arewa maso gabashin birnin Hama, kuma bayan sun shiga yankunan arewa maso gabashin wannan birni, sun ci gaba da shiga sauran bangarorin birnin naHama.
Babban kwamandan rundunar sojin kasar Siriya ya fitar da wata sanarwa da ke cewa, a cikin sa'o'i kadan da suka gabata da kuma yadda ake ci gaba da gwabza fada tsakanin sojojin kasar Siriya da 'yan ta'addar, duk da cewa an samu hasarar rayuka da dama, wadannan kungiyoyin sun samu nasarar ratsa da dama daga layukan kariya na birnin Hama da shiga wannan birni.
A cikin wannan sanarwa, an bayyana cewa, domin ceto rayukan fararen hula na birnin Hama, da kuma hana cutar da su a fadace-fadacen birane, sojojin na Syria sun sake girke kansu a wajen wannan birni.
Babban kwamandan rundunar sojin kasar Siriya ya jaddada kokarin da suke yi na kwato yankunan da ke karkashin ikon kungiyoyin 'yan ta'adda a bisa aikin da suke yi na kasa.
Idan dai ba a manta ba a safiyar yau Laraba 27 ga watan Nuwamba shekara ta 2024 ne 'yan ta'addar takfiriyya karkashin jagorancin kungiyar Tahrir Sham (tsohuwar kungiyar Al-Nusra) suka fara wani gagarumin farmaki daga yammacin birnin Halab inda suka samu nasarar kwace birnin na Halab da kuma garurwan yankunan kewaye a mataki na farko na mamayarsu A mataki na gaba, wadannan 'yan ta'adda na neman ci gaba zuwa wasu manyan biranen kasar Siriya.