28 Nuwamba 2024 - 12:28
An Kashe Sojojin Yahudawa Dubu 13 A Yaƙin Da Suka Yi Da Hizbullah Da Hamas

Shugaban kwamitin amintattu na majalisar malaman musulmin kasar Lebanon: An Kashe Sojojin Yahudawa Dubu 13 A Yaƙin Da Suka Yi Da Hizbullah Da Hamas.

Kamfanin dillancin labaran ƙasa da ƙasa na Ahl-Bait As ABNA ya habarta cewa: Haka nan kuma yayin da yake ishara da nasarorin da dakarun gwagwarmaya suka samu a yakin baya-bayan nan da kasar Isra'ila, shugaban kwamitin amintattu na kungiyar malaman addinin muslunci ta kasar Labanon ya bayyana cewa: Bisa labarin da aka samu daga hukumomin leken asirin kasashen yammacin turai, adadin waɗanda a kashe na sojojin gwamnatin sahyoniyawan a yaƙin da su kai a fagen ya nuna cewa; yakin na baya-bayan nan ya haura 13,000.

Sheikh Ghazi Hanina a yau Alhamis a wajen zaman makokin Yas Nabawi a birnin Qum, a cikin bayanan sa yayin da yake ishara da wasu misalan fatattakar da a kai gwamnatin sahyoniyawan a yakin da aka yi a baya-bayan nan, ya kara da cewa: Komawar Yahudawan sahyoniya zuwa mazauna arewacin Palastinu na daya daga cikin manufofin wannan yaƙi da gwamnatin Isra'ila ta kai kan Gaza da Lebanon Isra'ila ta gaza cimma wannan manufa. Lallai haramtacciyar kasar Isra'ila ta gaza kuma ta gaza wajen iya kare kanta daga makamai masu linzami da ake harba mata, ta gaza wajen kawar da kayan aikin soja na Hizbullah, ta gaza a kai harin ta na kasa da mamayar akalla kilomita hudu na kasar Lebanon.

Shugaban kwamitin amintattu na taron malaman musulmi na kasar Labanon ya bayyana cewa: gazawar Isra'ila wajen cimma manufofin da ta sanya a gaba ya sanya su kai hare-hare a wuraren zama da na fararen hula. Hakazalika gwamnatin sahyoniyawan ta gaza a manufofin yakin da take yi da Gaza, wanda shi ne ‘yantar da fursunoni da kuma halakar da kungiyar Hamas, kuma ba ta cimma manufarta ta hanyar guguwar Al-Aqsa ba, a karon farko yahudawan sahyoniyawan 200 da suke a yankunan da aka mamaye sun fada hannun gwagwarmaya, wanda ba a taba yin irin hakan ba a baya.

Shugaban kwamitin amintattu na taron malaman musulmi na kasar Labanon ya kira fitar bayanan sirri da dama na soji na gwamnatin Isra'ila a matsayin daya daga cikin nasarorin da dakarun gwagwarmaya suka cimma a yakin baya-bayan nan inda ya bayyana cewa: A wannan yakin a karon farko An kai hari kan sansanonin jiragen sama, sansanonin soji, masana'antu, da dai sauransu na gwamnatin Sahayoniya wanda Guguwar Al-Aqsa ta kore mafarkin yahudawan sahyoniya na kafa wata babbar Isra'ila tun daga kogin Nilu har zuwa Furat da kuma dakatar da yarjejeniyar karni da daidaita alaka da kasashen Larabawa.

Ya ci gaba da cewa: Malamai da dattawan kungiyar gwagwarmayar Musulunci 15 ne suka yi shahada a yakin da aka gwabza tsakanin kasar Labanon da gwamnatin sahyoniyawan, inda ya ce: Wadannan tsarkakakken jinin da aka zubar a kasa daga karshe ya kai ga samun nasarar gwagwarmaya. Tsagaita wuta da yarjejeniyar da aka yi tsakanin gwamnatin sahyoniyawan da kasar Labanon za ta haifar da alkhairai masu yawa ga bangaren gwagwarmaya, kuma hakan zai tilastawa firaministan wannan gwamnati wajen tsagaita wuta da Gaza.

A ci gaba da jawabin nasa yana mai cewa: Soyayyar Ahlul Baiti (AS) ba lamari ne na falsafa ko fikihu ga dukkan musulmi ba, sai dai lamari ne tabbatacce a cikin koyarwar addini.