27 Nuwamba 2024 - 10:34
Rahoton Irin Asarar Da Isra’ila Ta Yi A Ykinta Da Lebnon

Kafofin yada labaran yahudawan sun bayar da labarin hasarar rayuka da barnar da aka yi a yakin da suka yi da kungiyar Hizbullah

Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa na Ahlul-Baiti (AS) – ABNA- ya habarta maku cewa: Tashar talabijin ta 12 ta yahudawan sahyuniya ta bayar da rahoton cewa, yakin da aka yi da kungiyar Hizbullah a kasar Lebanon ya yi sanadin mutuwar 'yan Isra'ila 124 da suka hada da sojoji 79 tun bayan barkewar rikicin a cikin watan Satumba.

Gidan rediyon sojojin yahudawan sahyoniya ya kuma bayar da rahoton cewa, sakamakon hare-haren makamai masu linzami da na Hizbullah, an yi ta jin karar gargadi sau 22,715 a yankunan da aka mamaye. Fiye da gine-gine 9,000 da motoci 7,000 ne suka lalace gaba daya a arewacin Falasdinu da aka mamaye.

Majalisar ministocin yahudawan sahyoniya ta biya diyyar shekel miliyan 140 kwatankwacin dalar Amurka miliyan 38.4, wanda watakila zai karu saboda ci gaba da kwashe mutanen.