Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa na Ahlul Bait (AS) – ABNA-
ya habarta cewa, dakin gudanarwa na
kungiyar Hizbullah a cikin wata sanarwa da ya fitar ya bayyana cewa: Yayin da
yake tabbatar da kalaman mataimakin babban sakataren kungiyar ta Hizbullah
Sheikh Mujahid Naim Qassem dangane da shirye-shiryen dakarun makami mai linzami
na kai hari a kan duk wata kafa a cikin kasar Falasdinu da aka mamaye, muna
sanar da cewa wannan tsari gwagwarmayar ya dawo daram cikin karfinsa fiye da
karfinsa na da.
Dagewar da makiya Isra'ila suka yi wajen kai wa al'ummarmu masu daraja a kasar Lebanon hari zai sa Haifa da garuruwan da ba Haifa ba kamar Kiryat Shmona, Metula da sauran garuruwan da ke kan iyaka da kasar Labanon za su zama hadafin makami mai linzami, wannan shine abin da makiya suka gani a yau a Haifa da kewayenta.
Gwagwarmayar Musulunci tana gani tare da hangen da jin wurin da makiya ba su zato, kuma hannunta na iya kaiwa duk inda ta ga dama a cikin kasar Palastinu da aka mamaye, kuma wutar ba za ta tsaya ga rokoki da jirage masu saukar ungulu masu kai farmaki zuwa cibiyar sahyoniyawan ba.