Kamfanin dillancin labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (As) -
ABNA- ya habarto maku cewa: asibitin "Zif" da ke birnin "Safed"
da ke arewacin yankunan da aka mamaye ya sanar da karbar sojojin Isra'ila 39 da
suka samu raunuka a yakin da aka gwabza a kudancin kasar Lebanon.
A wani bangaren kuma tashar 12 ta gwamnatin sahyoniyawan ta bayar da rahoton cewa, sojojin Isra'ila 35 ne suka samu raunuka a yakin da suka yi da mayakan Hizbullah, kuma an bayyana cewa yanayin lafiyar wasu daga cikin wadannan da suka samu raunuka na cikin mawuyacin hali.
A sa'a guda daya gabata kakakin gwamnatin sahyoniyawan ya sanar da cewa an kashe sojojin wannan gwamnati 8 daga rundunar Golani da na Igoz a wani gumurzu da suka yi da dakarun gwagwarmaya a kudancin kasar Lebanon tun cikin daren jiya.
A safiyar ranar Talata 01 ga watan Oktoban shekarar 2024 ne sojojin kasar Isra'ila suka sanar da fara kai farmaki ta kasa a kudancin kasar Labanon kan mayakan Hizbullah.