21 Satumba 2024 - 19:31
Ministan Lafiya Na Kasar Labanon: Yawan Shahidan Ta’addancin Gwamnatin Sahyoniyawa Ya Kai Mutane 70

Ministan lafiya na kasar Labanon ya bayyana cewa: Adadin wadanda suka yi shahada sakamakon fashewar na'urorin sadarwa da kuma harin da aka kai a Dahiya da ke kudancin birnin Beirut ya kai mutane 70.

Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa na Ahlul-Baiti As - ABNA ya habarta cewa: ministan lafiya na kasar Lebanon Faras Al-Abyad a wani taron manema labarai da ya kira a yau asabar ya ce adadin shahidan hare-haren wuce gona da iri da gwamnatin yahudawan sahyuniya suka kai a yankunan kudancin birnin Beirut ya kai 31’ mutane uku daga cikinsu yara ne wasu bakwai kuma mata ne.

A ranar Juma'ar da ta gabata ce sojojin haramtacciyar kasar Isra'ila suka kai hari a yankin Dahiya da ke kudancin birnin Beirut tare da kai hari kan wani gini, lamarin da ya kai ga shahadar Ibrahim Aqeel daya daga cikin kwamandojin jihadi na kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon da kuma wasu 'yan kasar.

Ministan lafiya na kasar Lebanon ya kuma bayyana adadin wadanda suka jikkata a wannan harin mutane 68 ne kumana kai su zuwa asibitoci 12 kuma yanayin 2 daga cikinsu na da matukar cananta.

Ya ce: Saboda kasancewar gawawwakin da suka tarwatse da aikin fito da sauran da suke karkashin kasa da ba a kammala ba, adadin shahidan wannan ta'addanci yana karuwa.

Al-Abyad ya ci gaba da cewa: mutane 770 da suka jikkata sakamakon fashewar kayayyakin sadarwa a ranakun Talata da Laraba suna kwance a asibitocin kasar Lebanon, inda 152 daga cikinsu ke karkashin kulawar a sashen kula da marasa lafiya na musamman.

A ranar Talata, a wani mataki na aikata laifukan Ta’addanci gwamnatin sahyoniyawan ta tarwatsa wasu na'urori masu sadarwa a kasar Labanon. A cewar sanarwar da kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon ta fitar, ma'aikata da dama na bangarori da cibiyoyin Hizbullah ne suke yi amfani da wadannan na'urori.

An bayyana cewa, bayan fashewar na'urorin sadarwa na pager a kasar Lebanon a ranar Talata da yamma, a karo na biyu na tashin na'urorin sadarwa, an ji karar fashewar wasu abubuwa a yankunan kudancin birnin Beirut da wasu yankuna na kasar Lebanon. Bayan fashewar wadannan na'urori, gobara ta tashi a wasu gidaje da motoci da babura.

A cikin wadannan hare-haren ta'addanci guda biyu, gwamnatin Sahayoniya ta kashe akalla 'yan kasar Lebanon 37 tare da jikkata wasu fiye da 4,000 ta hanyar tarwatsa dubban na'urorin sadarwa marasa waya da wayoyin sadarwa.