Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa na Ahlul-Baiti
As - ABNA ya habarta cewa: an ji karar fashewar wasu bama-bamai a yankin Dahiya
na birnin Beirut da wasu yankuna na kasar Lebanon.
A cikin sabbin fashe-fashen da aka samu a kasar Labanon, baya ga wayar tarho, wayoyin hannu, na'urorin tafi da gidanka da wasu na'urorin sadarwa, wadannan fashe-fashen sun yi barna matuka.
Sakamakon wadannan fashe-fashe, an samu gobara da dama a gidaje, shaguna da motoci a sassa daban-daban na kasar Lebanon.
Ma'aikatar lafiya ta kasar Lebanon ta sanar da cewa mutane 9 ne suka yi shahada yayin da wasu sama da 300 suka samu raunuka sakamakon fashewar wasu abubuwa a yau a yankuna daban-daban na kasar Lebanon.
Idan dai ba a manta ba a yammacin jiya Talata 18 ga watan Satumba 2024 majiyoyin yada labarai sun sanar da faruwar wani lamari na tsaro ga dakarun Hizbullah na kasar Labanon a yankuna daban daban na wannan kasa da kuma kisan gillar da aka yi wa wadannan dakarun. Bisa labarin da aka bayar, an ce gwamnatin yahudawan sahyoniya ta yi nasarar kutsawa cikin na'urorin dakarun Hizbullah tare da tayar da wadannan na'urori, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutane 9 tare da jikkatar mutane 2,750.
...................................